12 ga watan Yuni za’a yi budurin da yafi na 29 ga watan Mayu – Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta yi watsi da ce-ce-ku-cen da ake yi kan rashin armashin bikin rantsar da shugaba  Buhari kuma rashin yi jawabi a wajen ratsar  dashi wa’adin mulkin karo na biyu da akayi a filin taro na Eagle Square da ke babban birnin tarayyar Abuja a ranar 29 ga Mayu.

Injiniya Buba Galadima, daya daga cikin manyan masu yawan sukar gwamnatin Buhari, ya ce rashin halartar shugabannin kasashen waje da tsoffin shugabannin Najeriya a wajen bikin ya nuna sun dawo daga rakiyar gwamnatin shugaba  Buharin ne.

Amma a yayin da yake mayar da martani, Babban mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu, ya shaidawa BBC cewa karya ce da hassada ta wasu mutane.

“Idan mutane sun girma shekaru sun kama su, ya kamata su daina karya domin za su koma ga ubangiji,” in ji shi.

Ya ce kwamitin shirya bikin ne ya bukaci shugabannin kasashen waje da duk wani bako daga waje ya bari har zuwa 12 ga wata domin halartar bikin ranar dimokuradiyya a Najeriya.

Garba Shehu ya ce kasashe 91 suka nuna sha’war halartar bikin rantsar da shugaba Buhari, kuma yawancinsu shugabannin kasashe ne da Firaminista.

Ya ce ministocin harakokin waje ne mafi kankantar bakin da suke tunani halartar bikin.

“Biki ne mai farin jini da mutane suke son su zo saboda kima da martabar Buhari.”

Ya ce akwai shugabannin da suka ce ko ba a gayyace su ba za su zo saboda shugaba Buhari.

Inda Gwamnatin Buhari ta ce doka ce ta ce a yi rantsuwa ranar 29 ga watan Mayu, shi ne dalilin rantsar da shugaban a ranar.

“Amma biki ya koma ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiya, wanda yanzu ya zama doka”

“Sojoji ne suka kafa ranar 29 ga Mayu, amma Buhari ya mayar da ranar zuwa 12 ga Yuni don kaucewa mulkin danniya da murdiya na soja.”

Ana dai danganta matakin da siyasa, domin farantawa wasu rai da suka dade suna bikin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga Yuni.

Sai kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya shaidawa OakTV cewa lokacin yin maganar shugaba Buhari bai yi bane, idan lokacin yayi to zai fito yayi magana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More