
2023: Koh wa zaiyi gwamnan Kano tsakanin Gawuna da Jibrin?
2023: Koh wa zaiyi gwamnan Kano tsakanin Gawuna da Jibrin?
Yawanci Gwamnoni idan sun gama zangon mulkinsu na karshe, sukan komowa su nemi sanata a mazabun nasu.
Hakan yasa magoya bayan Sanata Barau Jibrin suke share masa hanya akai yana da alaka ne da zaton da suke da shi ne na mai girma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, cewar zai iya zuwa ya nemi takarar kujerar sanatan Kano ta Arewa bisa al’ada.
Dan haka suke ganin ba wanda ya cancanci a musanya shi ya gaji kujerar Gwamnan kamar Sanata Barau Jibrin din duba da cewa shine sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa.
A daya bangaren suma magoya bayan mataimakin gwamnan jahar Kano dakta Nasir Yusuf Gawuna suna ganin shi yafi cancanta a matsayinsa na lamba Biyu, yayin da suke iza angizo da nuna bukatar ga mataimakin Gwamnan a nan gaba,domin kuwa mutum ne mai karamci tare da rikon amana, hakan yasa Gwamna ya dauko shi yana kwamishina akayi masa mataimakin Gwamna a zangon mulki na farko sannan kuma aka sake cin zabe dashi a zango mulki na biyu cewar su.
Sai dai wasu na ganin kamar ya yi wuri har a soma tunanin wanda zai gaji Gwamnan duba da cewa ko watannishida ba’a rufa ba da sake rantsar da Gwamna Ganduje a wa’adin mulki na na biyu.
Sannan kuma ga shari’ar gwamnan Ganduje da Abba Kabir na jam’iyyar PDP kan kujerar Gwamnar tana nan a kotu.
Amma duk da haka wasu na ganin ba wata matsala bace dan wasu sun fito suna nuna bukatar wasu da suke ganin sun cancanta su nemi takarar Gwamnan a 2023.
Ba yakin neman zabe bane kamar wani fatan alkhairi ne da suke musu wanda koda yaushe ana iya yi wa mutum a kowane lokaci.