2023:Kudancin Najeriya ya kamata a baiwa shugaban kasar – El-Rufai

Menene ra’ayinku game da hakkan?

Yayinda ake cigaba da tattaunawa kan wanda jamiyyar APC za ta baiwa tikitin takarar kujerar shugaban kasar Najeriya  a shekarar 2023, gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa kudu ya kamata mulki ya koma idan wa’adin mulkin shugaba Buhari ya kare.

Amma Nasir El-Rufai  bai bayyana wani sashen yankin kudu da  za’a baiwa mulkin ba.

Sai dai ya ce ba’a yi adalci ba idan har Arewa tace zata  cigaba da rike mulki idan  wa’adin mulkin Buhari ya a 2023.

El-Rufa’I  ya jagoranci kwamitin garambawul na jam’iyyar, inda ya bayyana cewa, duk da cewan kundin tsarin mulkin jam’iyyar bata tanadi raba dai-dai tsakanin Kudu da Arewa ba, akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsu wanda ke nuna a bawa  yan Kudun dama bisa adalci.

Gama-garin fahimta a fagen siyasar Najeriya shine ayi zagayen mulki tsakanin Kudu da Arewa, ba a rubuce yake ba amma kowa ya fahimci haka. Jam’iyyar  APC da gan-gan muka ki rubuta zagayen kujerar shugaban kasa a kundin tsarin mulkinmu, shine dalilin da yasa a shekarar  2015, Rochas Okorocha daga kudu maso gabas yayi takara, Sam Nda Isaih yayi takara, Buhari, Kwankwaso da sauransu sukayi takara.

Amma a matsayinmu na kungiya, ya kamata gamayyar yan jam’iyyar APC a Arewa mu zauna domin marawa mutum daya baya, musamman daga kudancin Najeriya  saboda bayan shekaru takwas na Buhari, ban tunanin shugaban kasa ya cigaba da kasancewa a Arewa sai dai idan akwai wani dambarwa inji  gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More