Gwamnatin Amurka ta taya Shugaba Muhammadu Buhari murnan sake lashe zaben 2019

A wata sanarwa mai dauke sa hannun Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ta yaba wa ‘yan Najeriya kan yadda suka fito suka kada kuri’unsu.”
“Muna sane da rahoton masu sanya ido na kasashen waje wadanda suka bayyana cewa zaben an yi shi cikin ‘yanci da adalci duk da cewa an dan samu tashe-tashen hankula nan da can.”
“Muna taya sauran ‘yan takarar da su ma suka fafata a zaben murna musamman yadda aka yi zaben cikin lumana.”
Haka kuma, sanarwar ta bukaci ‘yan kasar da su “tabbata sun yi sauran zabuka a mako mai zuwa cikin nasara,” in ji Mista Pompeo.

“The United States congratulates the people of Nigeria on a successful presidential election, and President Muhammadu…
Posted by U.S. Embassy Nigeria on Friday, March 1, 2019
Amurka ta ce a shirye take wajen gannin ta yi aiki da Najeriya don samar da zaman lafiya da ci gaba tsakanin kasashen biyu.
A ranar Larabe ne aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.

Ita ma kasar Faransa ta bi sahun Amurkan, inda ta taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben a ranar Alhamis.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More