Yadda rikici ya barke tsakanin Abdullahi Abbas da Abdulmumini Jibrin a Kano

Rikicin ya barke a tsakanin wasu bangarori na jam’iyyar APC mai mulki a jahar Kano inda har ta kai ga fitowa fila ana maidawa juna kalamai a bainar jama’a.

Dan majalisa wakilai mai wakiltar Mazabar Kiru da Bebeji wato Abdulmumin Jibrin, ya zargi shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas da kawowa APC matsala a jahar.

Abdulmumin Jibrin ya yi watsi da zargin da a ke yi masa na cewa ya yi wa jam’iyyar zagon-kasa inda ya ce, Abdullahi Abbas ya kamata a zarga da laifin shiryawa APC makarkashiya a 2019.

A wani faifai da ya shigo hannun Legit.ng Hausa, Jibrin ya yi barazanar tona asirin abubuwan da su ka faru a APC a zaben 2019 a dalilin yadda shugaban na APC ya ke jagorantar jam’iyyar ta su.

Jibrin ya yi kaca-kaca da shugaban na APC inda ya ce a dalilinsa ne jam’iyyar ta sha kasa a duk wuraren da ta rasa kuma har ta kai a ka yi kunnen doki a wajen zaben gwamnan Kano na 2019.

A cewar Hon. Abdulmumin Jibrin, gwamna Abdullahi  Umar Ganduje ya na da masoya, amma irin su Abdullahi Abbas ne su ka jawowa tafiyar APC bakin-jini har zaben gwamna ya kai wani zagayen.

‘Dan majalisar ya kara jaddada mubaya’ar sa na cewar ya nan daram tare da gwamna Abdullahi Ganduje dari-bisa-dari a Kano kamar yadda ya ke goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a sama, sai dai babban dan majalisar ya nuna cewa shugaban APC na Kano, ba zai iya masa wata barazana ba domin kuwa asali ma su ne su kayi kutun-kutun wajen ganin an sake nada shi.

Jibrin ya ce yayin da gwamna ya ke faman yi wa al’ummar jahar Kano aiki, babu abin da shugaban APC na jahar ya ke kokarin yi sai hada sa rikici da al’umma.

A karshe ya kara da cewa Abbas ba zai canja halin na saba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More