Babban jami’in da ya yi aikin zaben gwamna a jahar Kano a karamar hukumar Nasarawa, Farfesa Ibrahim Khalil Abdussalam ya bayyana gaban kotun da ke sauraron karar zaben da aka gudanar na 2019 a Kano.

Ibrahim Khalil wanda shaida ne ga jam’iyyar APC ya bayyanawa kotun da ke sauraron korafin zaben gwamnan Kano abin da ya sa a ka soke zaben Gama.

Farfesa Ibrahim Abdussalam ya sanar da kotu cewa sun lura akwai sabani ne a sakamakon zaben Unguwar Gama a lokacin da a ka yi zaben gwamnan Kano, hakkan  ya sa a ka nemi a gyara alkaluman kuma aka nemi  malamin zaben yankin ya koma domin gyara kure-kuren da a ka samu a Gama. Shaidan ya fadawa kotu cewa an samu hadin-kai tsakanin jam’iyyun da ke takara inda wakilin PDP da kan sa, Dr. Umar Tanko Yakassai ya amince a soke kaf zaben Gama domin ba su amince da shi ba.

A cewar wannan shaida da APC ta gabatar a kotu, Umar Tanko Yakassai, wanda ya tsayawa PDP a Nasarawa ya rubuta takarda da hannunsa a wata yarjejeniya domin a sake shirya wani zabe a Unguwar.

 

Daga baya ne kuma Umar Tanko Yakassai ya dawo ya fadawa hukumar INEC cewa ya tuntubi Lauyoyi wanda su ka nuna masa cewa bai da ce ba don haka ya ce ba ya goyon bayan a sake wani zaben. Wannan shaida ya kuma bayyana cewa Umar Tanko Yassai ya karbe takardar da ya sa-hannu a baya, ya keta ta. Farfesa

Abdussalam ya ce a na kokarin tattara kuri’un ne rikici ya barke a Nasarawa.

A cewarsa, saura kiris a fado da shi kasa inda wasu su ka zo su ka tattara sakamakon zaben daga teburinsa su ka yi gaba. Mai bada shaidan ya ce don dole ya ruga domin ya ceci ransa a zaben na Maris.

Lauyan da ke kare PDP, Eyitayo Fatogun, ya yi wa Farfesan tambayoyi a gaban kuliya. Jami’in na INEC ya tabbatar da cewa yarjejeniyar da jam’iyyu su ka yi, ba shi ba ne dalilin soke zaben na Gama. Yanzu dai APC ta gama gabatar da shaidun ta kamar yadda hukumar INEC ta kammala a cikin ‘yan kananin lokaci. An dage zaman wannan shari’ar jiya zuwa Yau Litinin 26 ga Agusta 2019.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More