Kalubalin sanata Gaya ga masu sukar shugaba Buhari

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu wato Kabiru Ibrahim Gaya ya bukaci mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya yi watsi da zargin dan majalisa na biyu, Junaid Mohammed yake yi akansa wanda ke cewa yana nuna son kai.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa sanata Gaya ya bayyana wa ma nema labarai hakkan ne a fadar Shugaban kasa a ranar Talata 22 ga watan Oktoba 2019, bayan wata ganawar su ta  sirri da Osinbajo a Villa, inda  ya bukaci Mohammed  yayi duba kan bayani kafin ya yi magana.

A kwanannan  ne rahotonnin suka  nuna cewa a Mohammed ya yi zargin cewa mafi akasarin mutanen da Osinbajo ya bawa  mukami sun fito ne daga kabilarsa da kuma mambobin cocinsa.

Gaya ya bayyana cewa Shugaban kasa da mataimakin Shugaban kasa sun cancanci mutuntawa daga dukkanin al’ummar  Najeriya.

Saboda yana da kyau a mutunta shuwagabanni da dattawan kasa,  karmar  shugaba Muhammadu Buhari, ba zai yiwu a fadi wani mummunan abu game dashi ko a zage shi ba saboda shi shugaban kasa ne.

Haka zalika matamakin shugaban kasar, babu wani amfani tayar da dukkanin wadannan zantuka.

Kafin Junaid ya yi magana, ya kamata ya duba tarihin wadanda ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More