DA DUMI DUMI:  Shugaba Buhari ya samu nasara a kotun koli

Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka yi na  kalubalantar nasarar shugaban kasar Najeriya  Muhammadu Buhari kan zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu 2019.

Kungiyar alkalan bakwai na babbar kotun da ta samu jagorancin Jastis Tanko Mohammed, shugaban alkalan Najeriya, tace, sun sakankance cewa babu wani amfani game da daukaka karar, hakkan yasa suka yi watsi da karar.

Jastis Tanko ya cewa, kungiyar alkalan ta duba tare da yin nazari akan shari’ar tun kusan makonni biyu da suka gabata, inda yace, za a sanar da dalilin watsi da karar a ranar da kotun zata saka.

Atiku da jam’iyyarsa na kalubalantar hukuncin ranar 11 ga watan Satumba ne wanda ya samu jagorancin Jastis Mohammed Garba a kotun sauraron kararrakin na zabe,yayin da karar ke kalubalantar nasarar Buhari kan  zaben shugabancin kasa da ya gabata.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More