A Ranar 15 ga Watan Janairu ne ake tunawa da Sojojin kasar Najeriya , kuma a irin rana ta yau aka kifar da gwamnati karo na farko a Najeriya. Haka zaluka kuma aka karbi sojojin yakin na basasa

15 ga Watan Janairu ce  ranar tunawa da Sojojin Najeriya da su ka riga mu kwanta dama.

Shugaba Buhari yayi magana da Sojojin Kasar da ke filin daga aka kuma yi ta’aziya ga wadanda suka rasu.

A  Rana irin ta yau ce ne aka kifar da Gwamnatin farko na Kasar, aka kashe Shugaba Tafawa Balewa da su Sardauna Ahmadu Bello.

A juyin mulkin ne manyan Sojojin Arewa irin su Laftana Pam, Laftana Largema, Kanal Kur, da Birgdiya Maimalari suka rigamu gidan gaskiya.

A kuma Rana irin ta haka ne ake tunawa da Sojojiin da aka karba daga Biyafara bayan sun shiga Yakin basasa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More