Yadda Sarki Sanusi ya ziyarci gwamna Ganduje a fadar sa

Shugaban majalisar sarakunan gargajiyan jahar Kano wato Sarki Muhammadu Sunusi II ya kai ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ziyara kwanaki kadan bayan kotun koli ta tabbatar masa da kujerarsa ta gwamnan jahar Kano.

Sarki Sunusi ya kai ziyarar ne a ranar Litinin 27 ga watan Janairu 2020 tare da babban basaraken jahar Edo, kuma Sarkin Bini Omo N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo Ewurare II Eheneden Erediauwa, inda suka hadu da gwamnan a fadar gwamnatin jahar Kano.

Premium Times ta ruwaito cewa sauran manyan sarakunan jahar Kano guda 4 sun riga sarki Sanusi  isa fadar gwamnatin jahar Kano, wanda hakkan yasa  tafiyarsu bata so daya ba,mai magana da yawun  gwamna Ganduje,Abba Anwar ne ya bayyana hakkan.

A yayin ziyarar da suka kawo fadar gwamnatin jahar, sabbin manyan sarakunan hudu sun gaisa da gwamnan daban daban, inda Sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar II ya fara gaisawa da gwamnan, sai Sarkin Rano, Tafida Abubakar-Ila.

Sarakunan sun taya gwamnan Ganduje  murnar nasarar daya samu a kotun kolin Najeriya  tare  yaba masa bisa kokarin da ya ke yi na shawo kan cutar zazzabin Lassa a jahar Kano.

Mun yaba da kokarin da gwamnatin jahar ke yi na shawo kan cutar Lassa, duba da kokarin gwamnatin, muna da yakinin an kusan shawo kan cutar.” Inji Sarkin Bichi.

Gwamna Ganduje ya bayyana godiyarsa ga Sarakunan, inda ya fara da yi ma marigayi Sarkin Kano Ado Bayero addu’a  tare da cewa, “ziyarar  mai cike da tarihi ce, domin  kujerar da ka zauna a kai, ita ce kujerar da mahaifinmu, marigayi Ado Bayero ya zauna a ziyarar daya kawo fadar gwamnati.”

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More