8 ga watan Maris ce ranar mata ta Duniya

A yau ake bikin ranar mata ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a kowacce shekara.

Taken bikin bana shi ne daidaita gudunmuwar maza da mata ga cigaban kasa, sai dai ana korafin har yanzu an yiwa mata nisa ta fannoni daban-daban na rayuwa.

Sai dai a yayin da ake wannan bikin, a Najeriya, sakamakon zaben Majalisar dokokin tarayya da aka yi a watan daya gabata ya nuna cewa Mata 6 ne kacal suka yi nasara a Majalisar datawa mai mambobi 109 ya yinda 11 ne suka yi nasara a majalisar wakilai mai mambobi 360.

Tuni dai wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin mata suka fara bayyana damuwarsu akan sakamakon zaben. Hajiya Saudatu Mahadi ta kungiyar WRAPA ta ce da irin wannan kadai aka kalla za a gane akwai jan aiki a gaba wajen tabbatar da daidaiton da ake son yi tsakanin mata da mata.

Wasu kasashen duniya sun dauki haramin a bukukuwa da zanga-zanga, da machi, da taruka, da shirya laccoci albarkacin ranar mata ta Duniya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More