A cire kayan aikin masu fyade – Gwamna El-Rufa’i

Menene ra’ayinku game da hakkan? Gwamna Nasir el-Rufai yana so a rika yi wa masu aikata fyaɗe dandaƙa

Gwamnan jihar Kadunan ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade ita ce yi wa masu aikata laifin dandaƙa.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom ranar Asabar.

An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.

Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More