A gida zan yi sallar Idi da iyalai na- Shugaba Buhari

Shugaban kasa Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, a gida zai gabatar da sallar Idi da iyalansa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na Twitter a yau Juma’a, 22 ga watan Mayu 20202.

Inda ya bayyana cewar, Shugaba Buhari zai yi Sallar Idi a gida ne don yin biyayya ga dokar hana fita da aka sanya a Abuja da kuma umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar na cewa kowa ya yi sallar Idi a gida. “Na dauki matakin ne bisa umarnin da Sultan na Sokoto kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayar na dakatar da yin sallar Idi a kasar baki daya, ” a cewar Shugaba Buhari.

A karshe kuma ya cewa wannan sallar Shugaba Buhari ba zai karbi bakoncin jami’an gwamnati ba, wadanda su kan kai masa gaisuwar Sallah – kamar yadda aka saba a al’adance.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More