A halin yanzu Najeriya na cikin takaici da bakin ciki – Obasanjo ya koka

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da yanzu haka ke cikin takaici da bakin ciki.
Tsohon shugaban kasar ya bayar da hujjar cewa duk da cewa kasar na da tarin arziki amma rashin kyakkyawan shugabanci ya sanya kasar gaza cigaba.
Ya fadi haka ne a ranar Alhamis lokacin da yake karbar wani littafi mai suna, ‘The Man, The General and The Presiden’, wanda Femmy Carrena ya rubuta, a dakin karatun Shugaban Kasa na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Obasanjo ya ce, “Addu’ata ita ce dukkanmu mu sami abin da za mu ba da gudummawa don mayar da kasar nan abin da Allah ya halicce ta ta zama – kasar da ke malala da madara da zuma.
“A yanzu, kasa ce da ke cike da dacin rai da bakin ciki, ba haka Allah yake so kasar nan ta kasance ba.
“Dole ne mu canza labari, dole ne muyi magana da kawunanmu cikin yaren wayewa.
“Babu inda za ka je a kasar nan da ba za ka ga masu hazaka a kowane sashe na kasar ba. Don haka, me ya sa za mu raina kanmu?.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More