A rage albashin masu rike da mukaman siyasa ba na ma’aikata ba kuma a siyar da jirage 8 ko 9 na shugaba Buhari wanda yake amfani da su – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya shawarci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sayar da jiragen da ke fadarsa domin a samu karin kudin tafiyar da harkokin kasa.

Atiku Abubakar ya bayar da shawarar ce sakamakon matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na rage kasafin kudin kasar saboda faduwar farashin man fetur a duniya.

Najeriya ta kiyasta kasafin kudin na 2020 ne bisa $57 a kan kowacce gangar mai daya amma annobarcoronavirus ta sa farashi ya yi muguwar faduwa a duniya, lamari da ya sa kasar ta rage kiyasin zuwa $30 kan gangar mai daya kuma hakan zai shafi kasafin kudinta na bana.

Sai dai a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis,tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce “abin mamaki ne a gare ganin cewa duk da faduwar farashin man fetur, da kuma gazawar Najeriya wajen kara samun kudin shiga daga bangarorin da ba man fetur ba, gwamnatin Najeriya ta yi ragi kadan na kasafin kudinta da kashi 0.6. Hakan na nufin an rage naira biliyan 71 kawai.” Ya kara da cewa hakan ya nuna cewa har yanzu Najeriya bata san mawuyacin halin da duniya take ciki ba. “Ya kamata a rage kasafin kudi mai matukar yawa na fadar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya. .
Dole a soke kasafin kudin da aka yi na saya wa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da sauran masu rike da mukaman siyasa motocin alfarma. “Kada a taba albashin ma’aikata, amma a rage albashin masu rike da mukaman siyasa. A sayar da jirage 8 ko 9 da shugaban kasa yake amfani da su”, in ji Atiku.

A cewarsa, ya kamata a soke kasafin kudin da aka yi wa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa don yin tafiye-tafiye. “Haka kuma ya kamata a soke kasafin kudin Naira biliyan 27 da aka yi da zummar gyara majalisar dokoki”, a cewar tsohon mataimakin shugaban Najeriya

Ya kara da cewa bai kamata a rage kasafin kudi da kasa da kashi 25 cikin dari ba domin kuwa ‘yan Najeriya ba za su so hakan ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More