A shirye nake na rattaba hannu kan hukuncin kisa da kotu tayi wa mawakin daya yi batanci ga Annabi- Gwamna Ganduje

Gwamnan jahar Kano Abdullahi Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu kan hukuncin kisan da wata Babbar Kotun Musulunci ta yi wa Yahaya Shariff Aminu, sakamakon samun sa da laifin batanci ga Manzon Allah SAW, idan mawakin bai daukaka kara ba.

Gwamna Ganduje ya ayyana haka ne a yayin wata ganawa da malamai da kungiyar Lauyoyi ta Kano da kungiyar lauyoyi Musulmi, da shugabannin hukumomin tsaro da ke jihar a yammacin yau Alhamis a Africa House da ke fadar Gwamnatin Kano.

Tun a watan Maris na 2020 Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda ya yi batancin a cikinta.

Gwamna Ganduje ya ce biyo bayan yadda al’ummar jahar da malamai ke ta matsin lamba kan ganin ya sa hannun a kan takardar hukuncin ya sa ya bayyana matsayinsa, amma ya ce tun da kotu ta bai wa Yahya Shariff kwana 30 dole sai a jira har sai wa’adin ya cika.

Haka zalika Gwamna Ganduje ya ce akwai bukatar malamai su ci gaba da wayar da kan al’umma don gudun samun rikici tsakanin kungiyoyin addini da ake da su a jahar.

Su ma dai kungiyar lauyoyi sun yi na’am da wannan mataki da gwamnan na Kano ya dauka, inda suka ce ya kamata al’umma su fahimci abun da doka ta ce kafin su yanke hukunci.

A ranar 10 ga watan Agustan da muke ciki ne wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a filin Hockey da ke Titin Gidan Zoo ta yanke wa Yahaya Shariff hukuncin kisan bayan ya amsa laifinsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More