A shirye muke mu karbe mulki daga hannun Buhari, inji PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana shirye shiryen karbe mulki daga hannun jam'yyar APC da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Wannan ya na kunshe a cikin kudurin taron gaggawa na Kwamitin Amintattun PDP da aka samu a ranar Alhamis.
A cikin kudurin wanda Sakataren Kwamitin Amintattu, Sanata Adolphus Wabara, ya sanya wa hannu, shugabannin PDP sun lura cewa rikicin da ya addabi jam’iyyar nan ba da jimawa ba za a warware shi.
Kudurin ya karanta, “Taron Kwamitin Amintattu ya duba kuma ya tattauna dalla-dalla, kamar yadda ya saba yi lokaci- lokaci, halin da Jam’iyyarmu PDP ke ciki a fadin kasar. Wannan taron gaggawa ya kasance mai matukar muhimmanci a wannan lokacin da ake tsaka da rikici na siyasa da tabarbarewar tattalin arziki a kasar, don tabbatar da zaman lafiyar dukkan gabobin jam’iyyar mu da kuma sanya su a faɗake da su kuma zama cikin shiri yayin da muke shirin sake karɓar ikon siyasa na ƙasa don amfanin ƙasa gaba ɗaya.
“Dangane da haka, taron ya amince tare da nuna godiya ga ayyukan da ke gudana na kwamitin sulhu da dabaru karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki…”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More