A Yanzu dai Abba K. Yusuf Ne Dan Takarar PDP A Kano – Hukumar INEC

A jiya Litinin 4 ga wata Maris  Hukumar Zabe ta INEC ta bayyana cewa, jam’iyyar adawa ta PDP nada dan takara a zaben da za a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris na kujerar gwamna a jihar Kano.

A safiyar jiya ne  kotun tarayya dake zama a Kano ta yanke hukuncin cewa, jam’iyyar PDP bata gudanar da zaben fidda gwani ba a jahar kano, saboda haka dan takararta na gwamna Abba Yusuf ba shi da hurumin tsayawa takara a zaben da za a gudanar.

A kan haka ne Maishari’ar ya umurci jam’iyyar PDP ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani a cikin mako biyu. Lauyan wanda yake karar, Kabiru Usman, ya ce, dole jam’iyyar PDP ta gabatar da sabon dan takara gwaman a zaben da za a gudanar.

A nasa tsokacin, lauyan jam’iyyar PDP, Bashir Yusuf, ya ce, hukuncin bai shafi takarar Abba Kabir ba a matsayinsa na dan takarar jam’iyyar PDP.

Wani dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Ali Amin-little, ne ya garzaya kotun inda yake kalubalantar tsarin da ta fitar da Abba Yusuf a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a jahar Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More