
A yau a ke kaddamar da majalisar dokoki ta 9 a Najeriya
A yau Talata 11 ga watan Yuni 2019 ne ake kaddamar da majalisar dokokin Najeriya wadda ta kunshi bangaren dattawa da ta wakilai.
Ana kuma sa ran zaben shugabannin majalisar.
Da dama daga cikin ‘yan majalisar dattawan da ‘yan majalisar wakilan sabbi ne, duk da cedwa akwai wayan da suka dade.
Majalisar dokokin Najeriya ita ce zuciyar dimokradiyya mafi girma a nahiyar Afirka don haka irin mutanen da ke cikinta ke gagarumin tasiri ko mai kyau ko marar kyau wajen tafiyar da kasa.
Wannan ne karo na tara da ake kaddamar da majalisar dokoki a kasar wadda ta hada majalisar dattawa mai kujeru 109 da kuma ta wakilai mai kujeru 360, a Najeriya.
A Yau ne sababbin ‘yan Majalisar Tarayya a Najeriyar za su sha rantsuwar kama aiki.
‘Yan majalisar za su maye gurbin wadanda suka gabatar da aiki ne daga shekarar 2015 zuwa 2019, kuma ita ce majalisa ta tara.