AAC tace magudin zabe akayi a Jahar Rivers

Dan takarar gwamnan jahar Ribas karkashin inuwar jam’iyyar AAC, wato Biokpomabo Awara wanda yake da goyon baya a gurin uban  gidansa  Rotimi Amaechi,ya bayyana cewar shifa murde masa zabe akayi domin wike ba shi yi ci zabe ba.

Ya kuma kara da cewa yana da sakamokon zaben na dukkannin guraren da aka gudanar da zaben na ranar Asabar 9 ga watan Maris 2019, yanda yake  da tabbacin cewa shine yake kan gaba da kuri’u 281,000, yayin da Wike  yake da  kuri’u 79,000.

Ganin hakan ne yasa hukumar INEC ta dakatar da zaben dan kada ni da magoya bayana mu cimma nasarar lashe zaben.

Bature zaben  ya bayyana wike a matsayi wanda ya lashe zaben dan samun damar kare shi  daga almundahanar da ake zargin shi dashi a lokacin da yake ministan ilimai na kasa.

Kuma na tabbata shugaban hukumar zabe wato Yakubu Mahmood, Kwamishinoni dake da hakkin kula da jahar Ribas, Bayelsa,Edo, May Agbamuche-Mbu, Obo Effanga da Etim Umoh duk suka goyon bayan shi inji Awara.

Awara kara da  bawa dukkanin magoya bayan sa hakuri, kuma ya gode musu bisa goyon bayan da suka nuna masa, tare da cewa kada suka karaya bada dadewa a su samu nasarar kwatar hakkin su.

A karshe yayi kira ga Wuke da jam’iyyar PDP na jahar Ribas da su dakatar da murnar lashe zaben da suke ganin su suka ci nasara, domin da sauran  “ Runa Akaba” inji Awara.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More