Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara Kotu kan zaben Kano

Alhamis 11 ga watan Afrilu 2019, Dan takarar gwamnan Jahar Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara  gaban kotun kararrakin zabe,kan zaben da aka gudanar na 23 ga watan Maris 2019 a kotun dake zaman ta a kan  titin Miller a cikin babban birnin jahar Kano.

Abba Kabir Yusuf, ya shaida wa BBC cewa, sun je kotun ne domin su gabatar da dukkan takardunsu na korafe-korafe da lauyoyinsu a kan zabukan da suka gudana na gwamna.

Dan takarar gwamnan ya ce, a zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa a jahar ta sanar da sakamakon inda ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ke kan gaba.

To amma daga bisani hukumar ta ce zaben bai kammala ba, inda aka sake yin wani a ranar 23 ga watan na Maris aka kuma bayyana dan takarar jam’iyyar APC, wato gwamna Ganduje a matsayin wanda ya samu nasara lashe zaben  bayan kuma kowa ya san duk abubuwan da suka faru a yayin zaben, in ji Abban.

Abba Kabir Yusuf, ya ce su a wajensu sam ba su yarda da sakamakon zaben da aka yi na biyu ba.

Ya ce, sun dauki matakin kin amincewa da sakamakon zaben ne saboda zabe ne wanda kowa a Najeriya ba ma a Kano kadai ba har da ma wasu kasashen duniya suka yi alla-wadai da shi.

Dan takarar gwamnan a jam’iyyar ta PDP a Kano, ya ce: “An yi zabe ne na son-kai, an hada baki da jami’an tsaro, kana an hada baki da su kansu jami’an hukumar zabe, an sassari wasu, an ji musu ciwo, sannan an ci mutuncin mutane.’

Bayan  wadannan abubuwa da aka yi, hatta wakilan jam’iyyu an kore su daga rumfunan zabe, sannan kuma cin mutuncin ma har ‘yan jarida ya shafa inji Abba

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More