Abubuwan da suka faru a APC darasi ne ga jam’iyyar

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta APC ta koyi darasi dangane da yadda aka gudanar da zabubbukan kasar ta Najeriya baki daya.

A wata hirar da ya yi da BBC ya bayyana cewa dauki dora ko kuma kakaba ‘yan takara na daya daga cikin abubuwan da suka kawo wa  jam’iyyar matsalolin data fuskanci a wasu jahohi wanda hakan ya yi sanadiyar rasa wasu kujerun gwamnoni da ma na ‘yan majalisar.

Ya bada misali da jahar Ogun inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi ungulu da kan zabo inda gwamnan jahar dan APC ne amma ya jagoranci wata jam’iyya domin ganin cewa an kada jam’iyyar APC a zaben gwamna.

Ya kuma ba da misali da jahohin karmar Imo, Bauchi da kuma Adamawa inda ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida ne suka yi sanadiyar faduwar jam’iyyar zabe a jahohin.

Ya yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki a kasar kan cewa a shekarar 2023 ta tabbatar an yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar sahihi kuma ingantacce a duk fadin kasar.

Farouk Adamu ya kuma yi hannunka mai sanda ga Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari inda ya ce ”shugaban ya ga yadda jama’ar kasar suka nuna masa soyayya a duk jam’iyyar da ya shiga har ya zama shugaban kasa don haka akwai hakkin mutane a kansa na ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta dore.”

Tun bayan nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben 2015 ta ke fama da rikice-rikicen cikin gida wanda hakan ya yi sanadiyar da dama daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Sai dai Farouk Adamu ya kara bayyana cewa za su ci gaba da zawarcin wadanda suka sauya sheka suka bar jam’iyyar APC domin ganin cewa an jawo su wurin ganin anyi tafiya daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More