Abunda Aisha Buhari ta tattauna da matar Goodluck a ziyarar data kai mata

Matar shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari ta karbi bakutar  matar tsohon shugaban kasar Najeriya Dame Patience Jonathan a ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu 2020 a fadar shugaba Buhari.

A haduwar tasu ne suka tattauna batun gudunmawar mata a siyasar Najeriya,ilimin yara mata da kuma aikin da matar Jonathan ke yi mai taken “Chanji Ga Mata”.

Aisha Buhari ta bayyana cewa sun tattauna  kan kokarin data keyi wajen ganin mata sun shiga harkar siyasa sosai da kuma gudunmawar mata a mulki, ta kuma ji  ra’ayin  Patience a lokacin mulkinta sannan kuma ta  saurari hangenta kan lamuran da ke addabar mata da yara a kasar.

A karshe ta bayyana jin dadin gama da ziyarar da ta kawo mata, tare da fatan kuma irin zaman a gaba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More