Abunda da dokar nada sabbin sarakunan Kano ta kunsa

Mai baiwa gwamna Ganduje shawara a bangaran  yada labarai Salihu Tanko Yakasai, ya ce dokar ta kunshi bai wa gwamna cikakkiyar damar nada Sarakuna da kuma masu nada Sarki wato (Kingmakers)

Dole ne kowacce masarauta ta mikawa gwamnatin jaha kasafin kudinta domin amincewa akan yadda za ta kashe kudin.

Gwamna na da ikon rage darajar kowane Sarki a Kano daga Sarki mai daraja ta daya zuwa mai daraja ta biyu ko ta uku ma, idan bukatar hakan ta kama, sannan zai iya tsige Sarki idan har Sarkin ya kauracewa zaman Majalisar Sarakunan Jahar Kano wadda za a kafa nan gaba, idan har yai hakan ba tare da wani dalili kwakkwara ba.

Sarakuna za su iya bai wa gwamnatin jaha shawara amma sai sun nemi izinin gwamnan.

Kowanne Sarki dole ne ya kiyaye yin abin da zai iya zubar da mutunci da martabar al’ummarsa a idon duniya.

 Gwamnan jahar Kano Abudullahi Umar Ganduje  ya rattaba  hannu a  kan sabuwar dokar ta kafa sabbin masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya bayan da majalisar jahar ta kada kuri’ar amincewa a ranar Alhamis.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More