Abunda GoodLuck ya fada a kan zaben Kogi da Bayelsa

Tsohon shugaban Najeriya dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya yi tsokaci game da tsarin zabe a lokacin kaddamar da wani littafi da aka yi a Garin Fatakwal da aka gudanar a ranar 14 ga Watan Nuwamba 2019. Tsohon shugaban kasar ya zargi ‘yan siyasa da laifin horas da yara da ake amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Goodluck yace yan siyasa na tura yaransu manyan jami’o’in na Duniya dan suyi karatu, sannan suyi amfani da yaran mutane yin bangar siyasa, dan kawo matsaloli a yin zaben na kasa tamu.
 
Tsarin zabe da na’urorin zamani shi ne zai kawo karshen magudi da murdiyar zabe da aka yi, idan kuma ba hakan ba, bata-gari ne za su cigaba da mulkar kasar.Inji GoodLuck.
 
Sannan kuma ya kalubalanci abubuwan da suke faruwa na takaice, inda ake amfani da yan dabar siyasa sunyin harbe-harbe, duba da cewa an shiga lokacin zaben Bayelsa da Kogi, ina ga ranar zaben.
 
A karshe yayi kira ga al’ummar Najeriya dama sauran kasashe masu tasowa su rungumi zabe ta hanyar amfani da na’ura domin a rage yawan magudi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More