Abunda gwamna Ganduje ya fada bayan bullar Coronavirus a Ka

Gwamna jahar Kano dakta Abdullahi Umar  Ganduje ya bayyana cewa, ya zama dole gwamnatin jahar ta dauki tsauraran matakai don hana cinkoson jama’a, duk da hakan zai iya takurawa al’ummar jahar.

Tuni dai aka killace wanda ya kamu da cutar ta covid19 mai shekaru 70 da haihuwa a asibitin dake kwanar Dawaki, inda gwamnatin jahar ta yi tanadi domin killace masu dauke da cuta.

Sannan kuma Gwamnatin jahar ta Kano ta ce zata rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jahar tare da tsaurara hana shiga da fita a kan iyakokinta bayan samun bullar cutar coronavirus a jahar ranar Asabar 11 ga watan Aprilu 2020, duk a yunkurin ta na dakile cutar ta Covid 19.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More