Abunda gwamna Ganduje yace gama da yaran da aka sata a Kano

Gwamna jahar Kano dakta Abdullahi Umar ganduje ya bayyana cewar zai iya bakin kokarin wajen ganin cewa ya kwatar wa yaran da aka sata a Kano aka siyar wa a Anambra hakkinsu.
Gwamnan yace, za a kafa kwamiti mai karfi da zai binciko tushen matsalar tare da hanyoyin gujewa afkuwar al’amarin a nan gaba.Inda ya yi alkawarin cewa duk wani matakin shari’a da ya kamata a dauka wajen ganin anyi wa yara 9 da aka sata din adalci gare su zai yi.
 
Sannan Ya yi kira ga iyayen yara da su dinga sanya idanu akan ‘ya’yansau tare da musu adddu’ar kariya daga miyagun mutane wajen gudun samun irin wannan matsalar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More