Abunda ke tsakanin Amina Zakari da shugaba Buhari

A ranar juma’a 4 ga watan Junairu ne  gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, babu wata dangantaka  tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Amina Zakari wadda aka nada a matsayin  shugaban cibiyar tattara zaben shugaban kasa mai gabatowa a watan Fabariru.

“Shugaban kasa Buhari ba shi da dangantaka ta jini tsakaninsa da kwamishinar  cibiyar tattara zaben shugaban kasar wato  Amina Zakari.”

Babban Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin yada labarai  Malam Garba Shehu,ne ya bayyana haka a Abuja “An dai samu auratayya ta nesa a cikin zuri’arsu amma cewa shugaban kasa na da dangantaka ta jini tsakaninsa da kwamishinar karya ce kawai,”in ji shi.

An nada Amina Zakari ranar Alhamis din da ta gabata,ta shugabanci Cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a hukumar  zabe mai zaman kanta wanda za a yi a watan Fabarairu mai gabatowa.

Matsayi da aka bawa Amina ya tayar da kura a siyasar Najeriya, inda jam’iyyar adawa ta PDP ke nuna cewa, Amina ‘yar uwar Buhari ce, kuma yadauke ne dan yi masa masa aiki .

Hakan yasa Sakataren watsa labarai na jam’iyyar  PDP ya soki lamirin nadin Amina Zakari da cewar yiwa  dimokaradiyya zagon kasa ne.

Sai dai Malam Shehu ya ce, maganar da jam’iyyar ta PDP ke yi, bata da kai kwatakwata.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More