Abunda ke tsakinin shugaba Buhari da Osinbajo

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin dake cewa akwai wani rashin jituwa a tsakanin ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na mataimakin nasa Yemi Osinbajo.

Babban mai ba Shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin majalisar dokokin tarayya, Sanata Babajide Omowurare ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin tarayya, yayi   martani ga masu sukar lamari wadanda suka dasa ayar tambaya akan hukuncin shugaba Buhari na sanya hannu a wata doka a Landan, Sanata Omowrare ya ce lallai kundin tsarin mulki ta ba Shugaban kasar damar aiki daga ko ina.

Ya yi bayanin cewa lamarin ya sha banban da na tsohon Shugaban kasa Umaru YarAdua da mataimakin sa Goodluckk Jonathan inda ta kai lokacin da tsohon Shugaban kasar baya iya aiwatar da ayyukansa saboda tsananin rashin lafiya.

Sai dai kuma ya yi gum da bakinsa kan dalilin da yasa Shugaban kasar bai aika wata wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar ba, inda zai mika ragamar aiki zuwa ga mataimakin Shugaban kasa.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kwana daya bayan ya rattaba hannu a gyararren dokar harajin hakar danyen man fetur dake cikin rafi a Landan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sallamar akalla 35 cikin hadimai sama da 80 a ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo. An tattaro cewa hadiman da lamarin ya shafa, wadanda aka baiwa takardar kama aiki a watan Agusta, sun hada wasu manyan hadimai na mussaman, masu bayar da shawara na mussaman, da hadimai na fasaha.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More