Abunda sarki Sanusi ya fada a gurin nadin sarautar Igbo

Sarkin jahar Kano Alhaji Muhammad Sanusi ya nuna goyon baya ga dokar kau da manufar da ke nuna wasu a matsayin baki wanda ke a fadin jahohin kasar ta Najeriya.

Sarkin  Sanusi ya bayyana hakan ne wajen taron  bikin cika shekara goma da nadin sarkin kabilar Igbo na Kano, wato  Igwe Boniface Ibekwe, ya bayyana ra’ayinsa na cewa yan Najeriya suna bukatar yanci iri guda wajen tabbatar da zaman lafiya a al’umma , nasara da kuma  cigaba.

Ya ce yan Najeriya suyi ma junansu da’a a jahohin da suke da zama ba tare da yin la’akari da yare, addini da kuma jahohinsu na asali ba.

A Kano bamu san da batun yan jiha na asali da wadanda ba yan asalin jahar ba.

An gina wannan birnin ne kuma arzikinta da ingancinta sun kasance akan budaddiyar yanayinta da masaukinta.” Ya bayyana cewa mutanen Kano ba su da nuna kyashi ko babancin yare ko na addini, inda yake jadadda cewa mutanen Kano na yanzu yawancin mutane ne wadanda asalinsu sun fito ne daga Gobir, Nupe, Kanuri, Babur, Jukun, da Wukari.

A karshe Ya mika godiya ga mai bikin da kuma sauran sarakunan gargajiya na sauran kabilu a jahar kan kokarin da suke yi wajen karfafa zaman lafiya tsakanin kabilu daban daban dake da zama a jahar ta Kano, tare da bukatar  al’umman Igbo da su cigaba da zaman lafiya tare da sauran yan Najeriya a jahar, inda ya jadadda cewa “Mu yan Najeriya ne,  kuma mun kasance yan adam masu fuskantar kalubale iri guda.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More