Abunda sassaucin dokar hana fita a Kano ta kunsa

Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sassauta dokar hana fita da Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya saka, ta tsawon kwanaki 14.

Hakkan yasa al’ummar birnin Kano za su iya fita a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, kamar yadda sanarwa ta bayyana.

Sai dai gwamnan ya ce manyan kantunan sayayya ne kadai za su bude, yayin da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Sannan ya ce za a sanar da sunayen kantunan da za su bude din a gidajen rediyon da ke jahar.

Har wa yau sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya zabi kasuwannin ‘Yan Kaba, Na’ibawa da ‘Yan Lemo su yi harkoki a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 zuwa 4:00.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More