
Abunda shugaba Buhari ya fada kan zaben Bayelsa
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya mista David Lyou na jam’iyyar ACP murnar zama gwamnan jahar Bayelsa, sakomakon zamun nasarar lashe zaben na ranar Asabar da aka gudanar a jahar Bayelsa.
Rahatunnin sun nuna cewa an samu rikici a wasu yankunan jahar.
Shugaba Buhari ya yaba wa magoya bayan jam’iyyar APC na jahar wadanda suka sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, dama sauran yan Najeriya. Inda yayi Allah wadai da rayukan da aka rasa ta sanadiyyar gudanar da zaben tare da yin ta’aziyya ga iyalan wadanda iftila’in ya afka dasu.
Sanarwar ta fito ne daga mai bawa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Femi Adesina.
Inda yace Buhari ya lura da kokarin da jami’an hukumar zabe da hukumomin tsaro suka yi wajen ganin an tabbatar da sahihin zaben da aka gudanar.