Abunda shugaba Buhari ya fada kan zaben Kogi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zaben gwamna  da aka gudanar a  jahar Kogi ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2019.

Shugaban kasar ya bayyana zaben da nasarar dan takarar jam’iyyar APC a matsayin kubuta da nasara mai kyau, yayin hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar  da yahaya Bello a matsayin ya samu nasarar lashe zaben a karo na biyu.

Inda ya yaba wa magoya bayan APC akan jajircewa da suka yi da tsayawa tsayin daka duk da lamari na rikicin da ya rika afkuwa a jahar a lokacin gudanar da zaben  na ranar Asabar.

Sanarwar ta fito ne daga mai bawa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Femi Adesina.

A karshe ya mika sakon ta’aziyyar sa ga yan uwan wadanda suka rasa ransu a zaben.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More