Abunda taron da gwamna Ganduje ya gabatar a Kaduna ya kunsa

Gwamna jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci taron karawa juna sani na Kwamishinoni, sakatarotin gwamnati tare da mayan jami’an gwamnati dan tattauna muhimman ayyuka da kudurorin gwamnatin ta jahar Kano, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar DFID-PERL (Hadin gwiwar yin aiki, samar da inganci da kuma karawa juna sani)wanda aka gabatar aka gabatar da a jahar Kaduna.
An gabatar da takardu na musamman akan maganar kudin shiga wato haraji inda shugaban hukumar kudaden shiga da kuma shugaban ma’iakatan gwamna Ganduje wato Ali Makoda suka gabatar, sai kuma muhimmiyar kasida da Farfesa Sagagi ya gabatar a kan tattalin arzikin jihar Kano da yadda zaa inganta shi.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, an gabatar da taron ne domin duk jami’an gwamnatin sa sun san inda gwamnatin sa ta dosa tare da yin aiki domin cimma nasarar hakan. Gwamnatin sa a wannan karo na biyu zata maida hankalin ne akan Ilimi wanda ya hada da na karatun tsangaya da kuma ganin cewa an daina bara a Kano, da ganin cewa kowanne yaro ya na zuwa makaranta tun daga matakin Primary har zuwa makarantun gaba da primary.

Sannan bangaren kiwon lafiya , wajen magance matsalar tare da ingantata tun daga matakin mazaba har zuwa jaha, da kuma bangaren aikace aikace domin ganin jahar Kano ta ci gaba fiye da yadda take a yanzu.

Taron ya samu halartar kakakin majalisar dokoki ta Jahar Kano Abdul’Aziz Garba Gafasa, Shugaban Jam’iyar APC Abdullahi Abbas, Sakataren Gwamnatin Usman Alhaji Shugaban Ma’iakata Ali Makoda ,manyan jami’an gwamnati da ma dai sauran su.

Gwamnan jahar Kaduna Mallam Nasiru El’Rufa’i shima ya hallarci taron tare da yin godiya bisa zabar jahar sa a matsayin wajen yin hahadar gabatar da taron.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More