Abunda taron da gwamnonin Arewa sukayi a jahar Borno ya kunsa

Gwamnonin shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta kwace ayyukan da aka ba ‘yan kwangilar da suka kasa ci gaba da gudanar da su a bai wa wadanda za su iya aikin cikin dan karamin  lokaci don ci gaban al’ummar yankin.

Kungiyar gwamnonin sun yi kiran ne a wani taron gwamnonin shiyar arewa maso gabas da suka gudanar a jahar  Maiguduri na kwana 2 wanda Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya jagoranta.

Taron ya sami halartar Gwamnonin jahohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da  kuma Yobe.

Kungiyar gwamnonin sun yaba wa gwamnatin tarayya tare da rundunar sojin kasar a bisa yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Sai dai sun yi kira ga sojojin da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da tashe-tashen hankula, ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da ta tabbatar da an mai da hankali sosai wajen jan ruwan yankin tafkin Chadi wanda al’umma da yawa ke amfani da shi.

Sannan kuma sun bukaci da a samar wa ‘yan sanda makamai na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Gwamnonin sun yi alkawarin yin aiki tare don ci gaban al’umarsu musamman wajen gano ma’adanan karkashin kasa, kamar su man fetur, iskar gas, harkokin noma da masana’antu.
Sannan sun yi alkwarin hada kai da gwamnatin tarayya wajen habaka makarantun tsangaya da karfafa karatun Islamiyya da na zamani da kuma hana yawon barace-barace a lasar ta Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More