Abunda ya haddasa rikicin Yarabawa da Hausawan Legos

Taho mu gama da ta faru tsakanin Yarbawa da Hausawa ‘Yan kasuwar Oke-Odo ya jawo kulle babbar hanyar da Legas zuwa Abeokuta, a jiya Lahadi 18 ga watan Agusta 2019.
Dukkanin motocin da suka nufi Legas daga Sango ta Jahar Ogun, da wadanda suke nufar Abule-Egba daga Oshodi da sauran sassan jahar sun tsaya cak babu motsawa.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar rikicin ya faro adaren Lahadi, lokacin da ‘yan kasuwar ke hada hadar saye da saidawar kayayyakin abincin, idan rikicin ya barke sakamakon dayan su ya buge daya yayin da suke dauke da kayan dako dukkanin su.

Yanayin ya kazanta sosai a safiyar Lahadin nan, inda fusatattun matasan Yarbawa suka rinka banka wa shagunan ‘yan Arewa wuta ba tare da kakkautawa ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More