Abunda ya haddasa rikincin kabilanci a jahar Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jahar Adamawa ta tabbatar da barkewar rikicin kabilanci a wani kauye na jahar.

Rikicin ya barke ne tsakanin Hausawa mazauna garin Tinno da kabilar Chobo da ke karamar hukumar Lamorde.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa wani karamin sabani aka samu bayan wani matashi ya kaɗe wani ɗan ƙabilar Chobo

Daga bisani `yan uwansa suka far ma mai babur din, inda shi ma wasu suka yi kokarin kare shi, kuma wasa-wasa rikici ya girma.

Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a cikin rikicin.

shaida ce, “Suna cikin mawuyacin hali saboda an yi masu kawanya ko ta ina sai dai ai ta jin karar bindigogi kawai.” Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar, DSP Sulaiman Yahaya Nugroje, ya tabbatar wa BBC da aukuwar rikicin, ko da yake ya ce yanzu ne suke tattara bayanan kan ainihin abi da ya faru.

Jahar ta Adamawa dai ta sha fama da rikicin kabilanci a baya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More