Abunda ya haifar da zanga-zanga a jahar Katsina

Mazauna kauyen ‘Yantumaki da ke jahar Katsina sun gudanar da zanga-zanga kan matsalar tsaron da yankin ke fama da shi.

Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna masu zanga-zangar da safiyar ranar Talata 9 ga watan Yuni, sun hau kan tituna suna kokawa kan yadda gwamnatocin tarayya da na jahar suka bar matsalar rashin tsaron tana ci gaba da tabarbarewa.

Matasan sun rika kona tayoyi da kuma allunan jam’iyyar APC mai mulki jahar don nuna rashin jin dadinsu game da matsalar dasuke fama na rashin tsaron.

Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da 8000 a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.

Hukumomi dai suna cewa suna daukar matakan shawo kan matsalar, amma masu lura da lamuran tsaro sun ce akwai bukatar a dauki karin matakai domin magance ta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More