Abunda ya kashe Mallam Isma’ila Isa Funtua

Malam Sama’ila Isa Funtua ya rasu ne sakamakon bugun zuciya ranar Litinin 20 ga watan Yuli 2020, a cewar daya daga cikin ‘yan uwansa.

“Mallam ya fadawa iyalinsa cewa yana son ganin likita amma sai da ya fara zuwa wajen mai aski. Daga nan kuma ya tuka mota zuwa asibiti,” in ji dan uwansa wanda ya bukaci a boye sunansa. Kamar yadda BBC ta rawaito.

 Isma’ila Isa Funtua dan kasuwa ne kuma jami’in gwamnati da ke da kwarewa sama da shekara 30, ya rasu yana da shekaru 78 a Duniya
Ana sa ran yin jana’izar mamacin a yau Talata.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa kan rasuwar amininsa Malam Isma’ila Isa Funtua wanda ya rasu ranar Litinin.
Inda ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban gibi, kasancewar ya taimaka masa musamman a tafiyarsa ta siyasa.

Shugaban ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwa da kuma al’ummar Jihar Katsina da ma sauran makusantan marigayin bisa rasuwarsa.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ji kan Malam Funtua, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai ba shi shawara kan kafafen yada labarai ya fitar ya bayyana marigayin a matsayin “mutum na kowa da ake matukar girmamawa.”

Fadar shugaban ba ta yi wani cikakken bayani ba game da dalilin rasuwarsa, amma an ruwaito makusantansa na cewa ya rasu ne sanadiyar bugun zuciya.

Malam Isma’ila Isa Funtua yana cikin manyan wadanda ake ganin suna da tasiri a gwamnatin Buhari.

Kuma tsakanin wata uku dai yanzu shugaban ya rasa manyan aminansa guda biyu bayan rasuwar Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadarsa da ya rasu watan Afrilu.
Marigayin ya taba rike mukamin minista sannan ya taba jagorantar kungiyar masu buga jarida ta NPAN na tsawon shekara takwas.

Shi ne ya assasa kamfanin Bulet International, babban kamfanin kere-kere da ya gina muhimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya.

Alhaji Isma’ila Funtua ne kuma daraktan gudanarwa na farko na jaridar Democrat.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More