Abunda yasa aka soke zaben Dino da Smart Adeyemi

Hukumar zaben mai zaman kanta wato INEC, ta ce zaben Sanata da aka gudanar a Kogi ta Yamma na ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2019 bai kammalu ba, kasancewar kuri’un da aka soke sunfi yawan wadanda ke kan gaba ya bada tazara.

Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ke kan gaba da kuri’u 80,118, yayin da mai bin sa Dino Melaye na jam’iyyar PDP ke da kuri’u 59,548.

Amma sai  dai, tun kafin bayyana sakamakon zaben ne  Dino Melaye yayi watsi da sakamakon da ake tattarawa.

Hukumar zabe,ta ce za ta saka ranar  da za ta gudanar da zaben na cike gibi.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More