Abunda zai sa a bude iyakokin Najeriya- Hameed Ali

Shugban hukumar Kwastam ta Najeriya, Kwanel Hameed Ali (ritaya) ya ce Najeriya ba za ta bude iyakokinta ba har sai lokacin da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita sun kaddamar da dokokin da ke dauke cikin yarjejeniyar shiga da fice na al’umma da kayayyaki na ECOWAS. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake da ya ke magana da manema labarai a ziyarar ya kai iyakar Idiroko na jahar Ogun. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

Shugaban kwastam ya ziyarci wurin tare da Shugaban hukumar shige da fice (Immigration) wato Muhammad Babandede, inda yace kaddamar da sharrudan shige da ficen kayyayakin zai tabbatar da samun riba da amfani ga dukkan kasashen da ke kasuwanci a tsakanin juna.

Bayan yabawa jami’an hadin gwiwa da ke aikin tabbatar da dokar na rufe iyakokin, Ali ya ce Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya gamsu da yadda ake gudanar da aikin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More