Abunda zaman da shugaba Buhari yayi da kungiyar ASUU ya kunsa

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa mambobin kungiyar malaman jami’a (ASUU) da su bayar da hadin kai a manufar yaki da rashawar gwamnati ta hanyar amincewa da manufofin na  tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS.

 Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin zaman da suka yi da shugabannin kungiyar malaman a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis 9 watan Janairu 2019.

 An samu labarin cewa  kungiyar ta ASUU na adawa da yiwa mambobinta rijista kan tsarin IPPIS, inda Shugaban kungiyar  ta ASUU wato Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana IPPIS a matsayin kutse wanda ya saba ma yarjejeniyar da ke tsakanin kungiyar da kuma gwamnatin.

 Sai dai hadiminsa shugaba Buhari wato Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali sosai wajen inganta jami’ai da tsarin makarantun jami’a ta yadda za a dunga yaye dalibai masu inganci, kamar yadda ya ba da tabbacinn cewa daga yanzu za a bawa ilimi kula na musamman a kokarin inganta kasar.

 A karshe shugaba Buhari ya bukaci mambobin ASUU da su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen cimma manufarta na inganta harkokin ilimi da samun sahihan takardun shaidar kammala karatu ta hanyar bawa shirin hadin kai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More