#Achecijamaa #ArewaMufarka – Aisha Buhari

Menene ra’ayinku game da wannan batun?

Uwargidan shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta  wallafa a shafin ta na Instagram  tana mai cewa,  #Achecijamaa da kuma #ArewaMufarka

Aisha Buhari sanya hotunan mijin ta shugaba Buhari tare da  hafsoshin tsaron Najeriya, inda ta yi amfani da wata  wakar da Adam Zango yayi wanda ke kokawa gama yadda ake fama da rashin tsaro, musamman a yankunan Arewacin kasar, inda ta sanya #Achecijamaa

Sannan ta kara sanya wata waka da mawakan kannywood ke yin addua’ar samun ragwame a gurin Ubangiji tare da yiwa shugaba Buhari addu’ar samun damar tafiyar da mulkinsa lafiya, sai wacce suka yi wanda ke yin kira ga mutanen Arewa da su tashi su farka tare da barin hassada da kyashin juna a tsakin, inda a nan ne sanya #ArewaMufarka
#OakTV #OakTVHausa
#OakTVOnline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More