
Adadin masu Coronavirus a Najeriya sun kai 276
Sabbin mutane guda ashirin da biyu sun kamu da cutar Coronavirus wacce aka sauya mata suna zuwa Covid 19.
Hukuma takaita yaduwar cuttuta ta Najeriya wato NCDC ce ta tabbatar da hakkan ranar Laraba 8 ga watan Aprilu.
Sabbin wanda suka kamun sune:
Mutane 15 a jahar legos, 4 a birnin Abuja, 2 a jahar Bauchi sai 1 a jahar Edo.
Daga karfe 9:00 na dare ne wayanda suka kamu da cutar suka kai adadin 276,yayin aka sallami mutane 44, 6 suka rasu.
Ga yadda jadawalin jahohin yake:
Lagos- 145
FCT- 54
Osun- 20
Oyo- 11
Edo- 12
Bauchi- 8
Akwa Ibom- 5
Kaduna- 5
Ogun- 4
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Benue- 1
Ondo- 1
Kwara- 2
Delta- 1
Katsina-1