Adamu Abubakar ya canza tasrin F-SARS

Sabon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu Abubakar ya soke rundunar nan dake yaki da ‘yan fashi da makami wato “Federal Special Anti-Robbery Squad” ko F-SARS a takaice.

Rundunar wacce tsohon Sufeto Janar Ibrahim Idris ya kafa da kuma ke karbar umarni daga Abuja tayi kaurin suna wajen take hakkin dan Adam.

Kafin yanzu dai F-SARS na karbar umarni ne daga hedkwatar rundunar ‘yan sandan kasar, da a baya har zangar zangar lumana ‘yan Najeriya suka yi don neman a soketa, bisa zargin cin zarafin jama’a, al’amarin da yasa mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbsjo lokacin da yake rikon mukamin shugabancin kasar ya bada umarnin ayi mata gyaran fuska.

Daga yanzu dai an soke wannan bangare na ‘yan sanda a matakin tarayya don haka an maidasu karkashin kwamishinonin ‘yan sanda ba jihohi.

Sufeto janar na ‘yan sandan ya yi gargadin cewa duk wani cin zali, sakaci ko ganganci da a kama  rundunar  da aikatawa  hakan to za a dora alhakin hakan ne a wuyan kwamishinan ‘yan sandan Jahar da abun ya faru.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More