AFCON: Najeriya ta yi na uku sakamokun doke Tunisia

A ranar Laraba 17 ga watan Yuli 2019 ne Odion Ighalo ya samu nasarar zura kwallo daya a ragar Tunisia, wanda hakan ya bawa Najeriya damar doke Tunisia a wasan neman na uku na gasar cin kofin kasashen Afirka.
 
Ighalo, wanda shi ne ya fi kowa cin kwallo a gasar bayan da ya zura biyar, ya ci kwallon ne bayan da golan Tunisia Moez Ben Cherifia ya kawar da kwallo daga hanyar dan wasansu na baya Yassine Meriah.
 
Sau takwas kenan Najeriya, wacce sau uku tana lashe kofin, tana zama ta uku a gasar.
 
Senegal za ta yi fatan lashe kofin a karon farko a tarihinta a wasan karshen da za ta fafata da zakarun 1990, Aljeriya a ranar Juma’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More