Afrika ta Kudu ta hana izinin tashen jirgin sama dan kwaso yan Najeriya

Wanda mataki ya kamata a dauka a ganin ku?

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta kawo wani sabon cikas ga kokarin kwashe yan Najeriya da rikicin kin jinin baki bakaken fata ya rutsa dasu a kasar Afirka ta kudu zuwa Najeriya, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito. Majiyar Legit.ng ta ruwaito a wannan karo gwamnatin kasar ta haramta ma jirgin Najeriya, Air Peace damar sauka a filin sauka da tashin na jirage domin kwashe rukuni na 2 na yan Najeriya da yawansu ya kai mutum 320.

Kamata ya yi jirgin Air Peace ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen Murtala Muhammad dake Legas tun a daren Litinin, amma har wayewar garin yau Talata 17 ga watan Satumba 2019 , kamfanin bai samu sakon izinin sauka a kasar Afirka ta kudu daga hukumomin kasar ba.

Idan za’a tuna a ranar Larabar data gabata ne kamfanin Air Peace ta kwashe yan Najeriya 178 daga kasar Afirka ta kudu, wanda ta dawo dasu gida Najeriya, amma ko a wannan lokaci sai da jami’an hukumar shige da fice na kasar suka yi kokarin kawo ma aikin matsala

Shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeam ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda yace duk kokarin da kamfanin ta yi na samun izinin sauka a kasar Afirka ta kudu hakan bai yiwu ba.

Bamu tashi da karfe 1 na dare kamar yadda muka shirya ba saboda rashin wannan izini, ma’aikatanmu sun jira har karfe 3 na dare suna jiran wannan izini, amma da muka ga abin ba yanzu zai zo ba, sai suka koma dakunansu a Otal, amma dai muna sa ran komai zai wuce. Inji shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More