Afrika ta Kudu ta ruki gafarar  Najeriya menene ra’ayin ku game da haka?

Afirka ta Kudu ta ruki  gafarar Najeirya a kan hare-haren kin jinin bakin da aka kai wa ‘yan Najeriyar da ke kasar.

Jakada na musamman na gwamnatin Afirka ta Kudu, Jeff Radebe, ya gabatar da takardar neman afuwar a madadin Shugaba Cyril Ramaphosa, a wata ganawa da yi da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jami’in na Afirka ta Kudu, ya shaida wa Shugaba Buhari a Abuja cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da aka samu, kuma ya ce tana daukar kwararan matakai.

Da alamu gwamnatin Afirka ta Kudu na kokarin kyautata alakarta da sauran kasashen Afirkan wadanda hare-haren kin jinin baki a Afrika ta Kudun ya shafa.

A yayin da Afirka ta Kudu ta dauki wannan mataki,  ita kuma Najeriya na ci gaba da kwashe ‘yan kasarta daga Afirka ta Kudu.

Ana sa ran isowar wasu  rukuni na ‘yan Najeriya 319 daga Afirka ta Kudu a filin jirgin sama da ke Legas a ranar Talata.

Sai dai Shugaba Buhari ya tabbatar wa jami’in cewa za a kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A makon da ya gabata ne ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Laraba cewa bayanan da ya samu sun nuna cewa ba a kashe dan Najeriya ko daya ba a rikicin.

Sai dai ya ce gwamnatin na duba yiwuwar yi wa jakadan kasar a Afirka ta Kudu kiranye tare da neman diyya ga sana’o’in Najeriya da aka lalata.

Najeriya dai ta janye daga Taron Tattalin Arziki na duniya da ya gudana a Afirka ta Kudu a makon da ya gabata bisa hare-haren.

Ta gargadi ‘yan kasarta daga “ziyartar wuraren da rikici ka iya barkewa” a Afirka ta Kudu har sai an samu zaman lafiya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More