Ahmed Lawan ya rantsar da okorocha a matsayin sanata

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawan, ya rantsar da tsohon Gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar jahar Imo ta Yamma a yau Alhamis 13 ga watan Yuni 2019.

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta baiwa Okorocha takardar shaida Sanatan lashe zaben Sanata a  mazabar Imo, wanda aka tsawon wata biyu ana jiran takardar shaidar.

Hakan yasa aka  tabbatar da Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 23 ga Fabrairu 2019.

Kotu ce ta bayar da umarnin cewa hukumar INEC ba tada hurumin hana  zababben Sanatan takardar shaidar lashe zaben.

Daga yanzu tsohon gwamnan zai wakilce jahar Imo ta Yamma  matsayin sanata

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More