Aikin N-Power: Majalisun Tarayya sun dakatar da shirin

Majalisun Tarayya a Najeriya sun dakatar da shirin gwamnatin kasar na daukar ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi 774,000 har sai sun samu cikakken bayani kan tsarin ɗaukar mutanen da za su ci gajiyar shirin.

Matakin ya zo ne kwana guda bayan karamin ministan kwadago Festus Keyamo ya yi zazzafar jayayya da ‘yan majalisar lokacin da suka nemi ya yi musu bayani yayin wani zama da suka yi ranar Talata.

Hadin gwiwar majalisar ƙwadagon ya bukaci sanin hanyar da aka bi aka zaɓo ayarin mutum 20 daga kowacce jiha a Najeriya don yin aikin tantance mutanen da za a ɗauka aikin na wucin gadi.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, zaurukan majalisar sun bukaci kwamitocinsu na kwadago su gayyato babban ministan ayyuka na kasar Chris Ngige ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban kwamitin kwadago na majalisar wakilai Hon. Muhammad Ali Wudil ya shaida wa BBC cewa damuwarsu ita ce gwamnati ta bijiro da shirin ne don amfanin jama’ar da suke wakilta, don haka suke bibiya don ganin an yi adalci da tabbatar da daidaito.

“Dole mu bibiya mu tabbatar da yadda aka yi aka zabo ayarin mutum 20 da za su yi aikin dauko matasan da za su ci gajiyar shirin,” in ji dan majalisar.

Ya ce sun nemi a dakatar da shirin ne saboda a matsayinsu na majalisa suna da hakki a yi musu bayani don su tabbatar an yi daidaito.

Ministan ya zargi ‘yan majalisar da kokarin karkatar da shirin da ofishinsa ya ɓullo da shi don cin moriyar masu karamin karfi.

Wasu rahotanni ma sun ambato Festus Keyamo na cewa jayayyar ta taso ne saboda ‘yan majalisar sun bukaci sai ya ba su ƙari a kan kashi 15% da ya ware musu tun da farko, abin da shi kuma ya ce ba za ta sabu ba.

Shi dai Muhammad Ali Wudil ya ce ministan ya shaida musu a yayin zaman ranar Talata cewa ‘yan majalisar ba su da ikon su tambaye shi game da yadda aka zabo mutanen da za su ɗauki ma’aikatan.

Sun nemi kashi 15% a cikin duk mutum 1,000 da za a ba aiki

Dan majalisar ya ce ba shi da wata masaniya kan zargin da ministan ya yi cewa sun nemi kashi 15% a cikin duk mutum 1,000 da za a duk ƙaramar hukumar Najeriya tsawon wata uku.

“A matsayina na shugaban wannan kwamiti, wallahi tallahi ƙarye ne. Ni dai ta bangarena bai ba da wani alkawarin kaso 15 ba. Kwata-kwata, ba ai haka ba,” cewar Ali Wudil. “Ba mu buƙata ba, shi kuma bai bayar ba.”

Ya kara da cewa idan ma haka ne, a matsayinsu na wakilan ‘yan Najeriya suna da ‘yancin gabatar da koke-koken jama’arsu don ganin sun shiga cikin wannan shiri don a dama da su.

Da aka tambayi Muhammad Ali Wudil ko me ya sa ba su yarda da buƙatar minista Festus Keyamo na ci gaba da zaman a gaban ‘yan jarida ba? Sai ya ce ai ba zaman sauraron ra’ayin jama’a ba ne.

“Idan public hearing ake yi, ana mitin ne a gayyato al’umma da kowa da kowa, wannan kam! Amma duk inda muke tradition din majalisa ne. Gwamnati da gwamnati, inda akwai wani abu da ake tunanin za a samu rashin jin daɗi ko rashin jituwa, sai mu tafi executive session.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More